07
Dec
Amorim ya zama kocin Man United na farko a wasan firimiya a gida da ya ci ƙwallo sama da biyu, karon farko da Man United ta zura 4-0 a bana a gasar. Manchester United ta doke Everton 4-0 a wasan mako na 13 a gasar Firimiya da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford. Marcus Rashford ne ya fara cin ƙwallo tun kan hutu, na shida da yake da hannu a cin Everton daga karawa ta takwas kenan. Bayan da suka koma zagaye na biyu Man United ta ƙarasa zura uku a raga ta hannun Joshua Zirkzee, sannan Rashford ya…
