Gobe za a yi jana’izar Pele

Daga BASHIR ISAH

Gobe Litinin za a yi jana’izar sarkin ƙwallon ƙafa na duniya, wato Pele, wanda ya mutu a ranar Alhamis da ta gabata.

Tsohuwar kulob ɗinsa a Brazil, Santos ce ta sanar da hakan a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, “Za a yi jana’izar sarkin ƙwallon ƙafa na duniya a Estadio Urbano Caldeira da ke Vila Belmiro.

“Daga Asibitin Albert Einstein za a dauki gwar zuwa babban filin wasa a ranar Litinin.”

Shugaban Ƙasar Brazil mai barin gado, Jair Bolsonaro, ya ba da hutun kwana uku don zaman makoki game da rasuwar marigayin.