‘Yan sanda sun tsare basaraken da ya yi lalata da ɗan shekara 14 a Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta kama wani basarake a Zariya da ya yi wa ɗan shekara 14 fyaɗe.

Kakakin rundunar Muhammadu Jalige wanda shine ya sanar da haka ranar Laraba, ya ce rundunar za ta maka basaraken a kotu da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike akai.

Da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labaran Nijeriya wani ɗan uwan wannan yaro, Hamza Zubairu ya ce basaraken ya yi lalata da ƙanensa ne ranar 9 ga Disamba a Unguwar Ƙwarbai.

Zubairu ya ce basaraken makwabcin su ne kuma kowa a unguwan na yi masa ganin dattijon arziki, ana daraja shi matuƙa.

Ya ce a wannan rana basaraken ya aiki yaron cikin ɗakinsa ya je ya ɗauko masa kuɗi kafin yaron ya ankare basaraken ya shigo ɗakin ya kulle ƙofar sannan ya zaro sharɓeɓiyar takobi ya nuna wa yaron.

Zubairu ya ce basaraken ya ce zai yanka yaron idan ya yi motsi ko ya yi ihu saboda abin da zai yi masa.
Ya ce da yaron ya fito sai ya ji tsoron faɗin abin da ya faru sai bayan kwanaki sai ya faɗi wa wata goggon sa.

“Bayan goggon yaron ta saurare shi sai ta kai ƙara ofishin ‘yan sandan Zariya.

Kodinetan cibiyar kula da waɗanda aka yi wa fyaɗe ‘Salama Sexual Assault Referral Center’ dake babban asibitin Gambo Sawaba a Zariya Aisha Ahmed ta ce cibiyar ta gudanar da gwaje-gwaje za ta miƙa wa ‘yan sanda sakamakon gwajin nan ba da daɗewa ba.