2023: Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taya ‘yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekara ta 2023.

Cikin saƙon nasa Buhari ya gode wa Allah da Ya ƙaddari ‘yan ƙasar da ke raye ganin wannan lokaci.

Ya yi fatan duka ‘yan Nijeriya da suka kwanta dama kafin sabuwar shekarar, mutuwa ta zama hutu a gare su.

Ya ce nan da wata biyar Nijeriya za ta samu sabon Shugaban Ƙasa da gwamnoni da sauransu.

Don haka ya sha alwashin gudanar da sahihin zaɓe ƙarƙashin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), don bai wa ‘yan ƙasa damar zaɓen shugabannin da suka dace.

Ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su guji duk abin da ‘yan siyasa ka iya aikatawa don haifar da tashin-tashina a cikin al’uma.

Sbugaban ya ce dole ne ‘yan ƙasa su haɗa kai da son juna ba tare da nuna wa juna bambanci kowane iri ba don zaman lafiyar ƙasa da cigabanta.

Haka nan, ya taɓo wasu manyan nasarori da gwamnatinsa ta samu sama da shekara bakwai da ya yi riƙe da mulkin ƙasa.