Daga WAKILINMU
Fadar Vatica ta tabbatar da cewa tsohon Fafaroma, Benedict XVI ya mutu yana da shekara 95 a duniya.
Rasuwar tasa ta ranar Asabar na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Fafaroma Francis ya yi kira ga Kiristoci da su yi masa addu’a saboda jikinsa ya yi zafi.
A cewar fadar ta Vatica, Benedict, wanda shi ne Fafaroma na farko dan asalin ƙasar Jamus cikin sama da shekara 1,000, ya rasu ne a gidansa da ke Mater Ecclesiae.
Ya kasance a cikin gidan dai tun lokacin da ya sauka daga mukamin nasa a shekarar 2013.
Sai dai fadar ba ta bayyana ainihin abin da ya yi sanadin mutuwar tasa ba, inda ta ce lafiyarsa ta taɓarɓare ne saboda tsufa.