Ganduje ya sallami Kwamishinan Addinai, Baba Impossible

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Gwamnatin Jihar ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Ganduje, ta sallami Kwamishinnan Harkokin Addinai na Jihar, Baba Impossible daga aiki.

Sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba, ya fitar a ranar Asabar ta nuna an dakatar da Kwamishinan ne saboda rahin biyayya ga tsare-tsaren gwamnati.

Ta kara da cewa, an samu Baba Impossible da yin gaban kansa wajen rage wa ma’aikatan da ke ƙarƙashinsa kwanakin aiki ba tare da izinin gwamnati ba.

Wato ya zabtare Laraba da Juma’a daga ranakun aiki wa ma’aikatan ma’aikatarsa.

Haka nan ba ya biyayya ga Gwamnatin sau da ƙafa.

Tuni dai Ganduje ya aike da sunan Dr. Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero ga Majalisar Dokokin Jihar Kano dan maye gurbin Baba Impossible.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *