Cristiano Ronaldo ya koma Saudiyya da wasa

Daga WAKILINMU

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan, Cristiano Ronaldo ya rattaba hannu kan kwatiragi da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya inda za a biya shi zunzurutun kuɗi miliyan £175 a shekara.

Ronaldo ya koma ƙungiyar Al-Nassr ne bayan ficewarsa da ƙungiyar Manchester United watan Nuwamban da ya gabata.

Ƙungiyar ta Al Nassr ta tabbatar cewa lallai Ronaldo ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da ita.

Yanke shawarar komawa Saudiyya ya kawo ƙarshen aikin gwarzon ɗan ƙwallon a matakin farko. Ana tunanin ya daɗe yana fatan ganin ya canza sheka zuwa kulob ɗin gasar Zakarun Turai wanda bai samu nasarar hakan ba.

Bayanai sun ce, taimaka wa Saudiyya samun damar ɗaukar nauyin Gasar Kofin Duniya a 2023 na daga cikin rawar da Ronaldo zai taka a komawa ƙasar da wasa da ya yi.

Ƙasashen Saudiyya da Masar da kuma Girka su ne ke zawarcin ɗaukar nauyin Gasar Kofin Duniya wadda za a yi a 2030.