28
Dec
Yanzu haka ƙungiyar Manchester City ta ƙasar Ingila tana cikin wani yanayi maras tabbas a gasar Firimiyar Ingila kuma babu wata alamar sassauci a nan kusa. Rashin nasarar da ta samu a ranar Asabar a hannun Aston Aɓilla 2-1 ya sa sun sauka daga 'yan huɗun farko cikin wasa takwas da ta buga. Saouthanmpton ce kaɗai ta fi Man City yawan wasannin da babu nasara cikin yawan wasannin, amma kuma idan ta samu maki ɗaya a wasanta na gaba bayan naɗa sabon koci Iɓan Juric, za ta kamo City a yawan maki. Hatta Wolves - da ta kori kocinta Gary…
