Liverpool ta yi wa Manchester united wankan jego

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta yi wa Manchester United aiki mai sauƙi inda ta lallasa ta da ci 7 rigis a wasan Gasar Premier a yammacin Lahadi.

Tauraron ɗan ƙwallon Netherlands Cody Gakpo, Mohamed Salah, da Darwin Nunez sun nuna bajinta matuƙa a filin wasa na Anfield, inda suka zura ƙwallaye biyu kowannensu a ragar abokan hamayyarsu ta Manchester.

Tawagar ta Jurgen Klopp dai sun kafa sabon tarihin nasara a fafatawar da aka yi tsakanin ƙungiyoyin biyu da suka fi samun nasara a gasar Ingila.

Kawo yanzu dai Mohamed Salah ya zama kan gaba a Liverpool a yawan cin ƙwallaye a Premier League a tarihi, inda ya zura ƙwallaye 129 a wasa 205 da ya buga.

Da wannan sakamakon Liverpool ta yi sama zuwa mataki na biyar da maki 42 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ita kuwa United wadda ta ɗauki Carabao Cup a bana tana ta uku a teburin da maki 49.