02
Apr
Daga MAHDI M. MUHAMMAD A daren Talata ne kaftin ɗin Argentina, Lionel Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a wasannin da ya buga na ƙasa da ƙasa, a karawar da ƙasarsa, Argentina ta lallasa Curacao da ci 7 da nema. Messi, wanda sau 7 ya ke lashe kyautar gwani na gwanaye a harkar ƙwallon ƙafar duniya, wadda ake kira Ballon d’Or, shi ya fara saka qwallo a raga a cikin minti na 20 da fara wasan da aka kara a birnin Santiago del Estero. Wannan na zuwa ne shekaru 17 bayan da ya fara ci wa Argentina ƙwallo a wasan…