Al-Hilal na zawarcin Messi kan biliyan N161.8 a shekara

Daga BASHIR ISAH

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Saudiyya, wato Al-Hilal, na zawarcin gwarzon ɗan wasan nan na Argentina, Lionel Messi kan kuɗi Dalar Amurka miliyan 385, kwatankwacin Naira biliyan 161.8.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da babbar abokiyar hamayyar Al-Hila ɗin, wato Al-Nassr ta saye shahararren ɗan wasan nan Cristiano Ronaldo.

Da alama dai, Saudiyya ta ba da himma wajen ganin ta mallake gwarazan da ake ji da su a duniyar ƙwallon ƙafa.

Domin saye Messi, dole Al-Hilal ta yi aman Dala miliyan $385, farashin da ake ganin ba kowa zai iya biya a kan ɗan wasan ba.

Bayanai sun ce, muddin Messi ya amince da tayin na Al-Hilal, dole ƙungiyar ta cimma yarjejeniya tsakaninta da PSG.

Ma’ana, dole ta biya PGS na Faransa kuɗinta kasancewar kwantiraginsa da PGS ɗin ba ta ƙare ba.

Masu fashin baƙi sun ce PGS ba za ta yi wa Al-Hilal da sauƙi ba wajen yarjejeniyar kasancewar ba ta shirya rasa Messi a matsayin ɗan wasanta ba.