‘Yan ta’adda sun kashe jami’an NSCDC bakwai a wajen haƙar ma’adinai a Birnin Gwari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan fashin daji ne sun kai hari kan jami’an hukumar tsaron farar hula, NSCDC, inda su ka kashe bakwai daga cikinsu a wani wurin haƙar ma’adinai, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Wata majiya ta shaida wa Daily Nigerian cewa ‘yan bindigar sun rasa mamba guda ɗaya a yayin wani artabu da ‘yan bindigar a wurin haƙar ma’adinai da wasu ‘yan ƙasashen waje ke gudanarwa a ƙaramar hukumar.

A cewar majiyar, tuni aka ajiye gawarwakin jami’an a asibitin ƙwararru na Barau Dikko da ke cikin babban birnin Kaduna.

Ƙaramar Hukumar Binrnin Gwari dai ta yi fice wajen fama da matsalolin varayin daji da masu garkuwa da mutane, inda suke cikin karensu ba babbaka a yankin, duk da jami’an tsaro suna cewa suna ƙoƙari wajen magance matsalolin tsaro a yankin da ma jibar bakiɗaya.