Gwamnatin APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka wa ‘yan Nijeriya – Buhari

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa a ƙarƙashin jam’iyyar APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗauka wa yan Nijeriya a lokacin yaqin neman zaɓe, saboda haka ya kamata ‘yan Nijeriya su zaɓi Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima, kuma jama’ar Yobe su sake zaɓar Gwamna Mai Mala Buni a karo na biyu tare da baki ɗayan ‘yan takarar jam’iyyar a babban zaven 2023 mai zuwa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ga cincirindon magoya bayan Jam’iyyar APC, ranar Talata a taron gangamin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa wanda jam’iyyar ta gudanar a filin wasa dake Damaturu, ya ce ‘yan Nijeriya su sake marawa jam’iyyar baya da Sanata Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, saboda su ci gaba da ingantattun ayyukan raya ƙasa da ya fara, bunƙasa tattalin arziki da ci gaba a fannin tsaro ga ƙasa.

Buhari ya ƙara da cewa ko da bisa dalilin ci gaban da aka samu a yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, a ƙarƙashin gwamnatin APC, fiye da kowane lokaci, al’amarin da ya zame alaƙalai ga haɗin kan Nijeriya, hujja ne ga ‘yan ƙasa.

Har wala yau, ya ƙara shaida wa dubban magoya bayan jam’iyyar irin mummunan ta’addancin da Boko Haram ya yi wa al’umma, ta hanyar ɓarnata dukiya da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa, kafin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro su fattatake su.

Da yake bayani kan muhimmancin neman ilimi, saɓanin aƙidar Boko Haram, shugaban ya ja hankalin iyaye a jihar Yobe da cewa, ‘‘ku tabbatar kun tura ‘ya’yanku makaranta, kuma ku yi ƙoƙari wajen fahimtar da su cewa duk abin da ka samu a duniya mai ƙarewa ne idan ba ilimi ba.

‘‘Saboda zan iya tuna maraicin da na yi; wanda ya jawo ban ga mahaifina da idona ba. Kuma na shafe shekaru 9 a makarantar kwana, saboda in nemi ilimi, wanda daga bisani na shiga aikin sojan Nijeriya.

‘‘Zan so ku jaddada imaninku, ku yi ƙoƙari wajen tafiyar da rayuwa kuma ku riqe ‘ya’yan ku da iyalinku cikin amana da gaskiya. Kar ku ha’inci ga wanda ya baku amana.”

Bugu da ƙari kuma, Shugaba Buhari ya gargaɗi ‘yan takara a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, a zave mai zuwa da cewa su tabbatar sun yi shugabanci nagari, kar su ci amanar talakawan da suka zaɓe su.

A hannu guda kuma, Jam’iyyar APC ta cika dukkanin alƙawuran da ta ɗaukar wa ‘yan Nijeriya, cikin shekaru takwas da suka gabata tana mulki a matakin tarayya, inda ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da inganta Nijeriya.

A nashi vangaren, ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da jam’iyyun adawa, su ci gaba da riqe taragon jirgin gwamnatin da Buhari yake tuƙawa.

‘‘Saboda wannan gwamnati ce ta masoya ci gaban ƙasa, masu mutunci da gaskiya.”

Haka kuma, ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, ya jinjina wa Shugaba Buhari a ƙoƙarin sa wajen dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas, inda ya yi alƙawarin ci gaba daga inda Buhari ya tsaya, tare da bunƙasa harkokin noma wanda zai mayar da yankin cibiya a Nijeriya.

‘‘Sannan kuma za mu baku ayyukan da za ku dogara da kanku. Kuma za mu farfaɗo da ayyukan noma, mu kori yunwa kuma mu baku duk abin da ya dace, mu ba ku tallafin kuɗaɗe don ku gina gidaje.”

Har wala yau, Tinubu ya yi alƙawarin idan ya kafa gwamnati yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ya zama tarihi, inda ya ƙara da cewa al’amarin da zai sanya ɗalibai za su kammala karatu cikin lokutan da suka dace.

A ƙarshe Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummar Yobe da Arewa maso Gabas su zaɓi ‘yan takarar APC a babban zaɓe mai zuwa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin da zai kafa za ta dawo da martabar tattalin arziki a Nijeriya.