Portugal ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin Belgium

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Portugal ta naɗa tsohon kocin Belgium, Roberto Martinez a matsayin sabon mai horasr da ’yan wasanta.

Martinez, mai shekaru 49, ya maye gurbin Fernando Santos, wanda ya ajiye aikinsa bayan da Portugal ta sha kashi a hannun Morocco a wasan daf da na kusa da ƙarshe na gasar kofin duniya.

Martinez ya ajiye aikin horar da Belgium ne bayan fitar da su daga gasar ta cin kofin duniya a Ƙatar a matakin rukuni, yana mai cewa ya yanke shawarar kawo ƙarshen wa’adinsa na shekaru shida ne tun a shekarun baya, dan haka da ma zai rabu da aikin, ko da kuwa tawagar ta sa ta zama zakara.

Sai da ƙasar Belgium ta zama ta 1 a duniya wajen iya ƙwallon ƙafa a ƙarƙashin jagorancin Roberto Mertinez, bayan da a suka kare gasar kofin duniya da ta gudana a Rasha cikin shekarar 2018 a matsayi na uku.

Tuni dai sabon kocin ɗan ƙasar Spain ya bayyana cewar zai tattauna da Cristiano Ronaldo kan makomarsa a tawagar ƙwallon qafar Portugal, daya daga cikin batutuwan da aka zura idanu ana dakon ganin yadda zai tunkara.

Bayan da aka tambaye shi ko zai cigaba da gayyatar Ronaldo domin wakiltar Portugal, sai Martinez yace yana yanke shawara kan ƙwallon ƙafa ne a filin wasa ba a cikin ofis ba. Dan haka zai fara ne da ganawa da dukkanin ’yan wasan Portugal 26 da suka halarci gasar cin kofin duniya a Qatar wanda kuma Cristiano na cikinsu.

Sabon kocin ya ƙara da cewar, Ronaldo ya shafe shekaru 19 yana cikin tawagar Portugal kuma ya cancanci a girmama shi.