Ga yadda albashin Lionel Messi zai kasance idan kulob ɗin Al-Hilal ta samu nasarar saye shi:
Shekara: Biliyan N161.8
Wata: Biliyan N13.4
Mako: Biliyan N3.3bn
Rana: Miliyan N481.7
Awa: Miliyan N20.7
Manhaja ta rawaito ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Hilal da ke Saudiyya na zawarcin ɗan wasan inda ta ce a shirye take ta biya shi Dalar Amurka miliyan 385 kwatankwacin biliyan N161.8 duk shekara.