Wutar lantarki ta yi ajalin ma’aurata da ‘ya’yansu a Zariya

Daga WAKILINMU

Aƙalla mutum huɗu sun mutu sakamakon wutar lantarki da aka kawo da ƙarfi a rukunin gidaje da ke Ƙofar Gayan a Zariya, Jihar Kaduna.

Wani ganau mai suna Malam Sagir Nata’atala, ya ce iftila’in ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Juma’a bayan da aka maido da wutar lantarki a yankin.

Ya ce marigayan ma’aurata ne sai kuma ‘ya’yansu biyu wanda dukkansu gobarar ta yi ajalinsu.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban Kwana-kwana na shiyyar Kaduna, Malam Umar Bello, ya ce gobarar ba ta rasa nasaba da tartsatsin wutar lantarki sakamakon maido da wutar da aka yi.

Wannan na zuwa ne bayan shafe kwana huɗu babu wutar lantarki a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *