Ganduje ya nemi ICPC, EFCC da Majalisar Tarayyar su binciki Hukumar Alhazai

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu (CSO), sun goyi bayan kiran da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi, inda ya nemi hukuma mai zaman kanta ta hukunta laifin cin hanci da rashawa da laifuka masu alaqa da hakan (ICPC), da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa  (EFCC), da kuma Majalisar tarayyar ƙasar nan a kan su yi bincike a kan hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) game da kuɗaɗen tafiyar da harkar alhazai na shekarar 2022, da kuma kwangilolin da aka ba hukumar.
 
Gwamna Ganduje ya yi wannan kira ne a a jihar Kano jim kaɗan bayan amsar rahoton aikin hajji na shekarar 2022 daga hukumar jin daɗin alhazaai ta jihar Kano, wanda Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, da kuma sakataren zartarwarta, Abba Dambatta suka jagoranta. 

A  cewar Ganduje, “Hajjin Bara na shekarar 2022 shi ne ma fi muni da na tava gani a tsahon zamana a kan kujerar Gwamnan Kano. An tafiyar da shi cikin halin riqon sakainar kashi, da rashin gaskiya da dama, da damfara da kuma kauce hanya”. Inji shi. 

Kuma ya ƙara da cewa, a sakamakon rashin iya aiki da gudanar da hukumar alhazan yadda ya dace, alhazai da dama sun sha baqar wahala, inda kuma hukumar ta yi musu halin-ko-in-kula. Kuma a cewar sa, ko wajen hidimta wa alhazan, hukumar ta faɗi wanwar.

Sai dai ƙungiyar ta gamayyar ƙungiyoyin wato CSO ta bayyana damuwarta a kan yadda makwanni suka shuɗe bayan kiran da Gwamnan jihar Kano ya yi na neman a binciki Hukumar alhazan, amma har yau majalisar tarayya ta kasa yin wani ƙwaƙƙwaran yunƙuri har yanzu don bincikar NAHCON don a samu a ceto hukumar daga rugujewa. 

Kodayake, ƙungiyar ta ce ta ji daɗin yadda hukumar ICPC ta shiga aiki nan-da-nan don bincikar manyan ma’aikatan hukumar alhazan a kan hajjin shekarar 2022 a kan kuɗaɗen gudanar da aikin hajji. Kuma a cewar sa, suna da labarin yadda hukumar ICPC ta gayyato wasu manyan jami’ai a vangaren ƙididdigar kuɗi da sashen kuɗin na hukumar.  

Laifuffuka da hukumar daƙile cin hanci rashawar ta tuhume su sun haɗa da zargin yin hawan ƙawara ga dokar gwamnatin tarayya ta alkinta kuɗaɗe, yin almubazzaranci a gida da ƙasar Saudiyya ba tare da neman izinin mahukuntan da suka cancanta ba. 

Haka zalika, daga cikin ɓangarorin da hukumar ta ICPC za ta bincika sun haɗa da kuɗaɗen da aka kashe wajen ba da muhallin alhazaai, abinci, magani da sufuri na aikin hajji 2022, sunaye da bayanai a kan kamfanonin da masu girki, da NAHCON ta ɗauka a aikin hajjin 2022, nawa ne kuɗaɗen kwangilar da kuɗaɗen da aka ba wa masu kwangilar da dai sauran abubuwa.