An naɗa Musulmin da ba ɗan jiha ba muƙamin kwamishina a Kuros Riba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A karon farko an naɗa Musulmi ba da ɗan asalin jihar ba tare da rantsar da shi a matsayin kwamishina kuma memba a majalisar zartarwa ta Jihar Kuros Ribas da ke Kudancin Nijeriya.

An naɗa Farfesa Ben Ayade, ya rantsar da Alhaji Adamu Uba Musa, Dr. Janet Ekpenyong, da wasu mutane goma sha ɗaya a matsayin sabbin kwamishinonin kula da harkokin gwamnatoci da lafiya a ranar Talata.

Bayan faruwar haka, Alhaji Musa ya zama Musulmi na farko da ba ɗan asalin jihar ba da aka naɗa a matsayin Kwamishina a jihar.

Gwamnan ya kuma yi amfani da wannan dama wajen shelanta wani qaramin sauyi a ma’aikatu biyu wanda ya kai ga Eric Anderson ya zama sabon kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a.

Sabbin kwamishinonin sun cika muƙaman da tsofaffin ma’aikatan su ne suka bar ko dai don neman muƙamai ko kuma suka yi murabus bayan sauya sheƙa da gwamnan ya yi zuwa jam’iyyar APC.

Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban ɗakin taro na ofishin gwamna da ke Kalaba, wanda ya samu halartar mataimakin gwamna, Farfesa Evara Esu, babban alƙalin jihar, Mai Shari’a Akon Ikpeme, Dr. Linda Ayade da sauran manyan jami’an gwamnati da baƙi.

Gwamna Ayade ya buƙaci sabbin kwamishinonin da su yi aiki tuƙuru domin ganin cewa gwamnatinsa ta kammala aiki cikin nasara.

Da ta ke mayar da martani a madadin sabbin kwamishinonin, Dr. Janet Ekpenyong wacce ta maye gurbin shugabar mata ta jam’iyyar APC ta qasa, Dokta Betta Edu, a matsayin kwamishiniyar lafiya, ta yabawa gwamnan bisa yadda “ya same mu mun dace mu haɗa kai da kai wajen ganin jihar Kuros Riba ta samu canji da kuma kawo sauyi a jiharmu domin ci gaban ɗaukacin ’yan jihar.”

Dokta Ekpenyong ta kasance kafin sabon muƙaminta, Darakta Janar na kula da lafiya a matakin farko na Kuros Riba, ta yi alƙawarin cewa ita da takwarorinta za su wakilci gwamnan da kyau a ma’aikatu daban-daban.