Raha nake yi, cewar matar da ta ce ta tara Naira biliyan guda da cinikoin ƙuli-ƙuli

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata matashiyar mai suna Angela Job Emodiae, wacce ta yi ikirarin cewa ta haɗa Naira biliyan guda a cinikin ƙuli-ƙuli, ta yi amanta ta lashe. Inda ta bayyana cewa ta faɗa ne kawai don saboda raha.  

Idan za a iya tunawa, a ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, 7 ga watan Janairun 2023 matashiyar mai suna Angela wacce take zaune a garin Jos ta jihar Filato, mamallakiyar kamfanin Anjees Food, ta wallafa a shafinta na dandalin Fesbuk cewa, ta haɗa Naira biliyan guda a kan cinikin ƙuli-ƙuli. Sannan ta ƙara da cewa, a wannan shekara ta 2023 kuma tana da burin haɗa fiye da Naira biliyan biyu. A cewar ta. 

A cewar ta, yawanci abokan cinikinta ‘yan Nijeriya ne mazauna ƙasashen waje, waɗanda suke yin odar ƙulin ta yanar gizo ita kuma ta tura musu ta hanyar masu jigilar kaya. 

Angela ta ƙara da cewa, har yanzu ba ta fara ɗiban kaya tana kai wa don sayarwa a ƙasashen waje ba. Amma tana yin ciniki ne a dandalin intanet musamman Fesbuk. Tana aika wa da waɗanda suka saya.

Akan shafin nata, ta wallafa wasu hotunan rasitai da hirar kafar sadarwa ta Wasaf, wanda ke nuna shaidar irin yadda abokan cinikinta suke biyan ta maƙudan kuɗi na kayanta da suka saya.  

Sai dai bayan wannan wallafar tata ta janyo ce-ce-ku-ce da yamutsa hazo a dandalin na Fesbuk, inda sai kuma Angela ta sake dawowa ta bayyana cewa, wannan zance dai ba wani abu ba ne illa labarin ƙanzon kurege, wanda ta ce ta yi shi a cikin raha. 

Sai dai duk da ta bayyana cewa, batun nata na baya ba gaskiya ba ne, amma wannan jawabin ma ya sa dubunnan ‘yan Nijeriya sake sarƙewa da sabuwar muhawara. Inda wasu suke ganin anya ba iya taku da tsaron kai ne ya sa ta sake dawowa ta warware wancan zance da ta fara yi ba? Allah dai masani.