A karon farko za a fara haska wasannin gasar Saudiyya a tashar DSTV

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan naɗa Cristiano Ronaldo a matsayin sabon ɗan wasan ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, hukumar gasar sun ƙulla yarjejeniya da DSTV don yaɗa wasannin gasar Larabawa a tashar DSTV.

Za a nuna gasar Larabawa ta talabijin a Channel 240.

Kowa zai iya kallon wasannin Al Nassr a tashar 240.

Wannan shi ne karo na farko a tarihi da za a nuna gasar wasannin Asiya ta talabijin a tashar DSTV.

A ɗaya ɓangaren kuma, Hukumomin Saudiyya na shirin kau da kai daga dokokin auratayya ta ƙasar domin yarjewa sabon tauraron ɗan wasan da ƙungiyar Al Nassr ta sayo wato Cristiano Ronaldo zama da farkarsa Georgina Rodriguez.

Dokokin Saudiyya dai sun haramta mace da miji da ba muharramai ba su yi rayuwa tare ba tare da aure ba.

To sai dai wata jaridar wasanni na ta ƙasar Spain (SPORTS) ta tuwaito cewa Ronaldo zai yi zaman daduro da Rodriguez a ƙasar Saudiyya kuma da alama ba za a hukunta su ba saboda karya doka.

Ronaldo ya koma Al Nassr ne daga Manchester United bayan da aka soke kwantiraginsa da kulob ɗin sakamakon wata hira da ɗan wasan na Portugal ɗin ya yi a watan Nuwamba da wani mai gabatar da shirye-shirye na Burtaniya, Piers Morgan, wanda ya caccaki club ɗin a ciki.

Ɗan wasan mai shekaru 37 ya yi kakkausar suka ga shugabannin Man United yana mai cewa babu wani ci gaba da ƙungiyar ta samu tun bayan tafiyar Sir Alex Ferguson. Ya kuma caccaki kocin United Erik ten Hag, yana mai cewa ba shi da mutunci.