APC Arewa Community tana taka rawar gani a Legas – Sa’adu Yusuf

Daga DAUDA USMAN a Legas

An bayyana cewar Ƙungiyar APC Arewa Community a Legas a ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙungiyar na jihar Legas Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma, tana taka rawar gani a Legas da kewayenta.

Shugaban ƙungiyar na Ƙaramar Hukumar Mailan dake cikin garin Legas Alhaji Adamu Abdullahi Abubakar ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan tashi daga taron da ƙungiyar ta APC Arewa kwaminiti ta shirya wa ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC tsohon Sanata Bola Ahmed Tinubu ‘yan siyasar Nijeriya gaba ɗaya domin goya masa baya a lokacin gudanar zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Taron wanda ya gudana a filin wasa na Onikan dake cikin garin Legas a ranar Lahadin nan da ta gabata.

Alhaji Adamu Abdullahi Abubakar ya cigaba da cewa haƙiƙa ƙungiyar tasu ta APC Arewa Community a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma tana taka rawar ganin a Legas domin kuwa ta shirya wannan taro ne domin nuna goyan bayant ga ɗan takarar shugabancin ƙasar nan Bola Ahmed Tinubu a game da takarar da yake yi.

Ya ci gaba da cewa Bola Ahmed Tinubu mutun ne mai kishin Nijeriya da kishin Arewacin ƙasar, ƙaunar al’ummar Arewa mazauna Jihar Legas.

Ya ce akan hakan ya ke ganin ya kamata ya bai wa ‘yan siyasar Nijeriya shawara a cewar sa musamman ‘yan Jam’iyyar APC dana sauran jam’iyyun ƙasar nan da matasa da su zavi jam’iyyar APC a matakin kujerar shugabancin ƙasar nan a lokacin zaɓuɓɓuka masu zuwa domin samun cigaban Nijeriya baki ɗaya.

Haka zalika ya cigaba da jinjina wa Shugaban ƙungiyar na APC Arewa Community a Legas Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma, a cewarsa bisa ga ƙoƙarinsa na haɗa kawunan al’ummar Hausawa da sauran ƙabilu ‘yan Arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas domin jadda danƙon zumunci da kuma cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ma’ana tare da bunƙasar harkokin kasuwancinsu a Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *