Za a fara aikin haƙo fetur a Nasarawa a Maris – NNPC

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ba da sanarwar shirinsa na fara haƙo fetur a Jihar Nasarawa a watan Maris mai zuwa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya snaar da hakan ga Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule, yayin da Gwamnan ya ya jagoranci wata tawagar jihar zuwa ziyarar NNPC a Abuja.

Kyari ya ce wannan ɓangare ne na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na gano fetur a sassan ƙasar.

Bayanin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Shugaban sadarwa na kamfanin, Garbadeen Muhammad, ya fitar ranar Juma’a.

“Dole a gaggauta aiwatar da aikin, saboda duniya na karkata daga amfani da fetur zuwa ga sauran makamashi.

“Ya fi mana alheri mu ci kasuwar tun kafin ta watse. In ba haka ba nan da shekara 10 babu wanda zai yarda ya zuba kuɗinsa a harkar fetur,” in ji shi.

Kyari ya ƙara da cewa, goyon bayan al’umma da kyakkyawan yanayi na da muhimmanci wajen samun nasarar aiwatar da aikin gudun kada a fuskanci irin matsalar da ake fuskanta a yankin Neja Delta.

A nasa ɓangaren, Gwamna Sule ya yaba wa Kyari kan nasarar da aka samu na fara aikin haƙo mai a Kolmani wanda Shugaba Buhari ya ƙaddamar a Nuwamba, 2022.

Mataimakin gwamnan, Dr. Emmanuel Akabe, masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Abdullahi Adamu da sauransu masu na daga cikin waɗanda suka mara wa Gwamna Sule.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *