Gwamnan Anambra ya roƙi Buhari ya saki Kanu, ya ce zai tsaya masa

Daga BASHIR ISAH

Geamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya roƙi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan ya hanzarta sakin jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ba tare da gindaya wani sharɗi ba.

Soludo ya yi wannan roƙo ne yayin da yake jawabi a wajen taron siyasa ranar Asabar a Awka, babban birnin jihar.

Ya ce, “Ina roƙo Gwamnatin Tarayya kan ta saki Mazi Nnamdi ba tare da wani sharaɗi ba. Ina son a sakar mini shi, zan tsaya masa.

“Muna da buƙatar Nnamdi Kanu domin tattauna matsalar a yankin Kudu maso Gabas. Dole mu murƙushe matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas, kuma muna buƙatar Nnamdi Kanu domun tattaunawa.

“A baya, mun kafa Kwamitin Sulhu domin gano tushen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar Kudu maso Gabas, kuma har ya kusa kammala aikinsa.

“Sai dai wannan matsala ta tsaro ba za a iya shawo kanta tare da shigo da masu ruwa da tsaki cikin batun ba,” in ji shi.

Idan za a iya tunawa, an tsare Kanu ne a Yunin 2021 a ƙasar Kenya inda aka maido da shi Nijeriya kan tuhume-tuhume masu nasaba da ta da ƙayar baya bayan da ya tsere ya bar ƙasar a 2017 bayan ba da belinsa.

A 2016 Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ba da umarnin tsare Kanu a kurkuku kan tuhumar ta’addanci.

Duk da dai Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta wanke Kanu daga tuhumar da ake yi masa a Oktoban 2022, amma gwamananti ta ƙi sakinsa saboda a cewarta, har yanzu yana da kashi a ɗuwawunsa.