Pele zai shafe lokacin Kiristimati a asibiti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shahararren da ƙwallon ƙafar duniya, Pele zai shafe lokacin bukukuwan Kiristimati a asibiti, kamar yadda iyali da likitocinsa suka bayyana, sakamakon magani da ake masa na cutar daji da ke ƙara ƙamari, da kuma matsalar ƙoda da zuciya.

Sanarwa daga asibin Albert Einstein na birnin Sao Paolo ta tabbatar da cewa Pele mai shekaru 82 na fama da matsalar zuciya da ƙoda, a yayin da ake mai maganin sankara, inda ta ƙara da cewa ba ya ɓangaren rai kwakwai, mutu kwakwai na asibitin.

Pele wanda ake wa kallo a matsayin ɗan ƙwallon ƙafar da ba a taɓa in yin kamarsa ba a duniya ya koma asibiti a birnin Sao Paulo a ranar 29 ga watan Nuwamba don a duba lafiyarsa da ta taɓarɓare tun bayan da aka mai tiyata a watan Satumban shekarar 2021.

A lokacin likitoci suka ce gwaji ya tabatar da cewa Pele, wanda ainihin sunansa, Edson Arantes do Nascimento yana da mastalar kwayar cuta a huhunsa, wadda ke jawo masa tangarɗa wajen numfashi.

A farko wannan wata, ’yayansa mata, Kely Nascimento da Flavia Arantes sun baiwa magoya bayansa ƙwarin gwiwa, bayan jita-jitar cewa yana cikin mawuyacin hali.