Wani ɗan Kenya ya mutu bayan faɗowa daga saman filin wasan Qatar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani ɗan ƙasar Kenya, ya mutu bayan da ya faɗo daga saman ginin filin wasan na Lusail da ke ƙasar Qatar.

Qatar da ke karɓan bakwancin Gasar neman kofin duniya ta sanar da soma bincike kan mutuwar John Njau Kibue mai shekara 24.

Bayanai sun ce matashin ya ji rauni sosai sakamakon faɗowar da ya yi daga saman ginin a ranar Asabar, jim kaɗan bayan da ƙasar Argentina ta lallasa Croatia a wasan kusa da ƙarshe na Kofin Duniya.

Rahotanni daga yankin sun ce, jami’an ba da agajin gaggawa ne suka fara duba John bayan faruwar hatsarin, kafin daga bisani aka ɗauke shi zuwa Asibitin Hamad inda a nan rai ya yi halinsa a ranar Talata.

Masu shirya gasar sun ce sun sanar da ’yan uwan marigayin kan halin da ake ciki, inda suka bada tabbacin za su miƙa duk wani haƙƙin sa ga ’yan uwansa.