Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shahararren ɗan wasan gaban Portugal, Christiano Ronaldo ya bayyana cewa, bayan cimma yarjejeniya da ƙungiyar Manchester United, ya raba gari da ita ba tare da ɓata lokaci ba.

Ronaldo ya ce, “ina son Manchester United, kuma soyayyar da nake yiwa magoya baya ba za ta sauya ba.”

Ɗan wasan na Portugal ya ce, barin ƙungiyar ya zo masa a daidai, don haka zai cigaba da mayar da hankali a fagen ƙwallon ƙafa.

Sanarwar da Ronaldo ya fitar a shafinsa na Instagram, ya ce, yana yiwa tsohuwar ƙungiyar tasa fatan samun nasarori a nan gaba.

Wannan matakin dai ya zo ne bayan maganganun da ɗan wasan ya furta a baya-bayan nan, game da alaƙarsa da mai horar da Manchester United Eric Ten Hag.

Hakazalika, ɗan wasan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, ya ce ƙungiyar da ke buga Premier Ingila ta ci amanarsa, abin da ya haifar da cece-kuce daga ɓangarori daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *