20
Jan
Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana jin daɗinsa tare yaba wa 'yan wasan Super Eagles dangane da nasarorin da suka samu a duka wasanni ukun da suka buga a gasar cin kofin Afirka (AFCON) da ke gudana a ƙasar Kamaru. Buhari ya nuna jin daɗinsa ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na facebook a ranar Laraba. Buhari ya buƙaci 'yan wasan da su ci gaba da tabbata a kan wannan hanya ta nasara da suka ɗauka har zuwa ƙarshen gasar tare kuma da zama jakadu nagari ga Nijeriya a cikin filin wasa da kuma wajen…