14
Sep
Kano Pillars ta yi nasarar doke Ikorodu United 3-0 ranar Lahadi a wasan makon farko da fara gasar firimiyar Nijeriya ta 2024/25. Pillars ta buga wasan ne a jihar Katsina, bayan da ake gyaran filin wasanta na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Nijeriya. Pillars ta ci ƙwallayen ta hannun Mustapha Umar da Rabiu Ali da ya zura biyu a raga, mai shekara 43 yana buga kaka ta 18 a babbar gasar tamaula ta Nijeriya. Da wannan sakamakon Pillars, wadda ake kira sai masu gida tana ta ɗaya a kan teburi da maki uku, sai Sunshine Stars ta…
