Daga NASIR S. GWANGWAZO
Cibiyar Horti Nijeriya wacce take samun kulawar IFDC da take samun tallafi daga ƙasar Neitherland, domin bunƙasa noman kayan lambu, musamman tumatur, albasa, kabeji da kokwanba, ta gudanar da wani taro na tallafa wa mata guda 2,000 a jihohin Kano da Kaduna, waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi daban-daban na jahohin.
Cibiyar dai ta shiga ƙauyuka daban-daban, inda ta nemi ƙungiyoyi manoma mata kuma ta tallafa musu da yadda za su dogara da kansu, don samun bunƙasar arziki.
Horti Najeriya ta tantance ƙungiyoyin da suka fi nuna ƙwazo a yayin da suka baje fasahohi daban-daban na gudanar da ayyukansu na noma.
Abdullahi Umar jami’i ne a IFDC a ƙarƙashin Horti Najeriya, ya bayyana wa manema labarai cewa, shirin nasu sun kasa shi gida huɗu, inda kashi na farko shine a Kano da Kaduna.
“Munufar ita ce mu na so mu ga cewa an sami ilimi na zamani yadda za a yaɗa noman kayan lambu a Kano da Kaduna, domin aƙalla a na so manoma 60,000 su amfana ta yadda za su sami yalwar arziki.
“Kasha na biyu kuma yana Oyo da Ogun, inda aƙalla mutane 2,000 ne su kuma za su amfana da manufarmu ta na so mu cike giɓin da yake tsakanin Arewa da Kudu kuma a samar musu da Kasuwa.
“Kashi na Uku magana ce ta tallafi da samar da jari, domin su yaɗa abinda suka koya ga sauran al’umma.
“Kasha na huɗu magana ce ta kasuwa, domin a ba su ilimi sun iya sun noma sai a yi musu haɗi na kasuwa domin su samu cigaba da ilimin da aka koya musu,” inji shi.
Taron dai ya samu halartar wakilai daga Ma’aikatar Gona Ta Jihar Kano da Jami’ar Ahmadu Beollo da ke Zaria da sauran jami’ai daga sassa daban-daban.
