CNTAC: Haramcin da Amurka ta sanya wa kayayyakin Xinjiang ya sava dokokin ciniki

Daga CMG HAUSA

Ƙungiyar kare muradun kamfanonin samar da tufafi na ƙasar Sin CNTAC, ta ce haramcin da Amurka ta sanyawa dukkan kayayyakin da ake samar a yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai na ƙasar Sin, ya saɓa wa dokokin cinikayya da tattalin arziki na ƙasa da ƙasa.

CNTAC ta ce, tana adawa mai tsanani game da matakin Amurka na haramcin da ta sanya, wanda ba kawai yana haifar da mummunar illa ga moriyar kamfanonin saka tufafi na ƙasar Sin ba ne, har ma zai haifar da illoli ga tsarin dokokin kamfanonin saka tufafi na duniya.

A cewar ƙungiyar ta CNTAC, audugar Xinjiang, wacce take da matuƙar daraja da samun karɓuwa a duniya, ta kasance a matsayin kashi 20 bisa 100 na jimillar audugar da ake samarwa a duniya, kuma tana da matuƙar muhimmanci game da tasirin samar da dawwamman ci gaba ga kamfanonin saka tufafi na ƙasar Sin da ma na duniya baki ɗaya.

Ta kara da cewa, yunƙurin Amurkar tamkar nuna kiyayya ne da neman danne haƙƙoƙin kamfanonin saka tufafi na ƙasar Sin, ƙungiyar ta ce matakin yana matukar haifar da mummunar illa ga tsaro da zaman lafiyar kamfanonin, da ma tsarin hada-hadar cinikayyar kamfanonin saka tufafi na ƙasa da ƙasa, kuma yana lahanta moriyar ma’aikatan kamfanonin saka tufafi na ƙasa da ƙasa.

Mai fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *