DA ƊUMI-ƊUMI: Babban jami’in Kwastom ya rasu yayin gurfana a Majalisar Wakilai

Wani babban jami’in kwastom ya rasu a asibitin majalisa dake Abuja.

Marigayin baƙo ne da yazo majalisa domin amsa kiran da majalisa tayi wa hukumomin gwamnati dake tara haraji.

Yana cikin tambayar ‘ƴan majalisa sai ya faɗi. An kaishi asibitin cikin majalisar cikin gaggawa inda rai yayi halinsa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar ya fitar, Akin Rotimi, yace yana sanar da al’umma rasuwar jami’in kwastom da ya gurfana gaban majalisar. Sabida mutuntawa ba zamu faɗi sunan jami’in ba.

Leave a Reply