Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafi ƙarƙashin NSIPA

Spread the love

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da dukkan shirye-shiryen ba da tallafin da ke karkashin kulawar Hukumar Shirin ba da Tallafi ta Kasa (NSIPA).

A cewar Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Taryya, Segun Imohiosen, an dauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da bincike yadda ya kamata kan zargin almundahana a hukumar.

Sanarwar ta ce, Fadar Shugababn Kasa ta bayyana cewa, an dakatar da baki daya shirye-shiryen bayar da tallafi guda hudun da ke karkashin NSIPA, na tsawon makonni shida.

Shiryen-shiryen da lamarin ya shafa sun hada da Shirin N-Power, Shirin Conditional Cash Transfer, Shirin Government Enterprise and Empowerment da kuma Shirin Ciyar da Dalibai na Grown School Feeding.

Imohiosen ya kara da cewa, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa matuka kan matsalolin da ke tattare da biyan masu cin gajiyar shirye-shiryen hakkinsu.

Ya ce, an kafa kwamiti na musamman tare da dora masa aikin gudanar da bicike mai zurfi kan yadda hukumar ta NSIPA ke gudanar da harkokinta.

Bugu da kari, ya ce har zuwa lokacin da za a kammala wannan bincike, an dakatar da dukkan ayyukan NSIPA.

By Editor