Fostin ɗin da ɗan wasa Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na Instagram na cewa matarsa ta samu ‘juna biyu.
Wannan shi ne fostin na farko da wani ɗan wasa a duniya ya samu mabiya (Likes) mutum miliyan 27 da dubu ɗari ɗaya, kuma yana ci gaba da ƙaruwa ahalin yanzu ashafin Instagram.
Ba a iya ƙwallon ƙafa ba, a kowane irin wasa a duniya babu wani ɗan wasa da ya taɓa samun yawan mabiya da suka kai na waɗanda suka bibiyi fostin ɗin na Cristiano Ronaldo wanda ya wallafa a jiya tare da shi da matarsa Georgina.