Gargaɗin Buhari: Ku daina min bambaɗancin tazarce

Daga SANI AHMAD GIWA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi masu yekuwar kamfen ɗin tazarcensa bayan 2023 da su daina kuma su shiga taitayin su, domin babu haka a tsarin sa.

”Da Alƙur’ani na yi rantsuwa kuma shekara huɗu sau biyu duka sai da na yi rantsuwa cewa iya shekarun da zan yi kenan, saboda haka kada wani ya bijiro da abinda ba shi cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan. Ba zan lamunce wa duk wanda ya bijiro da haka ba.”

A cikin takardar wadda Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya gargaɗi masu kokarin bijiro da tazarcensa a lokacin da yake ganawa da wata tawagar ‘yan Nijeriya mazauna kasar Saudiyya, bayan kammala taron ƙasa da ƙasa na zuba jari da ya gudanar a ƙasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi ba yin tazarce ba ne a ransa, yayin da ya nuna jin daɗinsa yadda aka fito da kimiyyar yin zaɓe da na’urar ‘Card Reader, wanda ya ce Allah ya amsa addu’ar sa, kuma hakan zai magance maguɗin zaɓe kamar yadda aka yi masa har sau uku a baya, a cewarsa.

“Bayan maguɗin da aka yi min har sau uku a zaɓukan da suka gabata, na ce ‘Allah na nan’, wasu suna min dariya, sai Allah ya amsa addu’a ta aka zo da sabon tsarin gudanar da zabe da na’urar ‘Card Reader’ a lokacin, kuma babu wanda ya isa ya saci ƙuri’a ko ya saya,” inji shi.

Buhari wanda ya kammala ziyarar aiki da ya kai Ƙasar Saudiya, kuma ya yi sallar Juma’arsa a Babban Masallacin Madinah, ya ce zai ci gaba da kiyaye Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da kuma hukunta duk wanda ya nemi yi wa dokar ƙasa karan-tsaye.

Shugaban ya kuma bayar da tabbacin cewa zai yi iya kar ƙoƙarin sa wajen ganin ya inganta rayuwar ‘yar Nijeriya cikin watanni 18 din da suka rage masa a wa’adin mulkinsa.
“Zan yi duk abinda zan iya yi don ganin na kyautata rayuwar al’umma da kuma gina ƙasar.”

Haka kuma, Shugaba Muhammadu Buhari ya gargaɗi ‘yan Nijeriya mazauna Ƙasar Saudiyya su zama wakilai nagari wajen nuna kyawawan halayen ƙasar su.

Ya kuma yi kira da jama’an Nijeriya musamman ‘yan adawa, da su duba irin ƙalubalen tsaron da Nijeriya take ciki a shekarar 2015 a Arewa maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu, daga bisani sai su auna su gani irin ci gaban da aka samu a halin yanzu.

“Abinda ke ci min tuwo a ƙwarya shi ne kashe-kashen mutane da garkuwa da su da ‘yan bindiga ke yi a Arewa maso Yamma. Saboda haka mun ɗauki kwakkwaran mataki akan su kuma za mu ci gaba da jajircewa har sai mun ga bayansu,” inji shi.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kuma roƙi ‘yan Nijeriya mazauna Ƙasar Saudjyya da su kasance masu bin doka da oda, da kuma kiyaye dokokin ƙasar, kada su gurɓata kyakkyawar alaƙar da aka jima ana cin moriya tsakanin ƙasashen biyu.

Ambasadan Nijeriya a Ƙasar Saudiyya, Yahaya Lawal da kuma Babban Jami’in tuntuɓa na Jeddah, Ambasada Abdulkarim Mansur, sun bayyana cewa akwai ‘yan Nijeriya da suka haura miliyan 1.5 da ke zaune a Ƙasar Saudiyya.

A cewar su, “‘Yan Nijeriyan suna iya bakin ƙoƙarin su wajen nuna kyakyawan halaye da kuma bin doka da oda a Saudiyya.”