Dabarun kimiyya da nacewa bin ƙa’idoji ne jigon shawo kan annobar COVID-19 a Sin

Daga SAMINU HASSAN

Masana kiwon lafiya na hasashen cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da wanzar da nasarorin da take samu, a yakin da take yi da annobar COVID-19, duk da sake ɓullar cutar da ake samu a wasu sassan ƙasar a baya bayan nan.

Tun ɓullar wannan annoba a ƙasar yau shekaru 2 da suka gabata, mahukuntan ƙasar sun aiwatar da matakai daki daki na dakushe bazuwar ta, waɗanda suka yi matukar tasiri wajen dakushe kaifin ta. Babban sirrin nasarar da ƙasar ta cimma ya zuwa yanzu dai shi ne nacewa bin dabarun kimiyya, da bin ƙa’idojin masana, ta yadda ƙasar ta kai ga cimma daidaito tsakanin matakan yaƙi da annobar, da kuma bunkasar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Wasu daga masu fashin baki, game da yanayin bazuwar annobar COVID-19 na ganin cewa, abu ne mai wahala cutar ta bace baki ɗaya cikin ƙanƙanin lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yanayin ɓullar sabbin nau’o’inta a sassan duniya daban daban. Don haka dabarun kimiyya da Sin ta aiwatar tun da fari, kama daga matakan kandagarki zuwa na rigakafi, da ƙa’idojin ba da tazara, da taimakawa sauran sassan ƙasashen duniya da kayan yaki da annobar, da alluran rigakafi, sun yi matuƙar tasiri wajen rage kaifin bazuwar cutar a cikin gida, da ma sauran sassan duniya.

Kamar yadda Sinawa kan ce “Nasara na samuwa ne bayan juriya”, ƙasar Sin ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, wajen ɗaukar dukkanin matakai da suka wajaba, ta kuma rungumi manufar tabbatar da yaƙar cutar baki ɗaya. Karkashin wannan manufa, kawo yanzu, ana ci gaba da gudanar da gwajin cutar, da bin diddigin waɗanda suka yi cudanya da masu ɗauke da ita, tare da sanya ido matuƙa wajen jagorancin dukkanin ayyukan yaki da cutar.

Ko shakka babu, irin waɗannan matakai da tuni suka yi tasiri a nan ƙasar Sin, kamata ya yi su zamo abun misali ga sauran sassan duniya, dake fuskantar yaɗuwar wannan annoba, wadda kawo yanzu ta yi mummunar ɓarna, ga yanayin tattalin arziki da zamantakewar al’ummun duniya baki ɗaya.