Dariye da Nyame: Ya kamata Buhari ya san cewa dukiyar Nijeriya ba ta shi ba ce – Hajiya Naja’atu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohuwar ‘yar a mutum Buhari, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a watan Afrilu ya yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke faɗin ƙasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya riƙe kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar Naira biliyan 1.16, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar Naira biliyan 1.6, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

A wata tattaunawa da Radio France International, RFI a ranar Litinin, wacce Daily Nigerian ta saurara, Naja’atu Mohammed ta ce ya dace Buhari ya gane cewa dukiyar Nijeriya ba ta shi ba ce.

Naja’atu ta ce a jiharsu ya dace a yafe musu, “ya kamata gwamnonin jihohinsu su yafe musu ne, saboda a can suka aikata rashawar, don kundin tsarin mulki ya bayar da yafiya ne ga jihohin da aka aikata laifuka.”

Ta ƙara da cewa yafe wa tsofaffin gwamnonin yana nuna cewa ba a shirya kawo ƙarshen rashawar Nijeriya ba. Ta ce kotu ta tabbatar da zargin da ake musu don haka yafiyar na nuna cewa ba a yaƙi da rashawa a ƙasar nan.

“Gwamnati ta yi kuskure. Ya dace Shugaban Ƙasa ya gane cewa dukiyar al’umma ba ta shi ba ce. Gwamnatin Tarayya ba ta da damar yafe wa waɗanda suka tafka laifi a jihohinsu.

“Abu na biyu shi ne wannan yafiyar ta Buhari tana nuna cewa gwamnati ta gaza. Wannan shi ya sa muke fama da rashin tsaro. Satar biloniyoyin Filato wacce kotu ta tabbatar, ba za ta rasa alaƙa da kashe-kashe, taɓarɓarewar ilimin jihar, lalacewar titina da kashe-kashen da jihar take fama da shi ba.

“Bayan EFCC da kotu sun gama iyakar ƙoƙarinsu tsawon shekaru, bai dace kawai ka yafe wa masu laifin ba. Ba kuɗinka suka sata ba. Me ya sa gwamnatin Buhari ta ke yin yadda ta ga dama?”

Ta ce a tarihin Nijeriya ba a tava mulki mai rashawa da sata kamar na mulkin Buhari ba.

A cewarta kundin tsarin mulki bai bayar da damar yin wannan haukar ba. Idan haka ne ya kamata a yafe wa ‘yan ta’adda. Saboda babu ta’addancin da ya zarce satar da gwamnonin suka yi.

Ta ci gaba da cewa an zaɓi Buhari ne don ya yi yaƙi da rashawa, amma yanzu shi ne ya ke yafe wa masu rashawar.

Alamu na nuna cewa Buhari ba abin amincewa ba ne, inji ta. Ta ce a tarihi ba a taɓa gwamnatin da ta fi ta Buhari rashawa ba a ƙasar nan. A cewarta satar da ake yi ta zarce tunani.