Hisba ta aske gashin ɗaliban da suka yi askin banza don murnar gama makaranta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta kai wani samame babbar Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin Tofa, inda ta kama wasu ɗalibai da askin banza a kansu, domin murnar kammala karatun sakandire.

Dakarun Hisba ɗin sun yi nasarar damƙe da dama daga cikin ɗaliban, waɗanda su ka yi askin da a ke wa laƙabi da “ba kwaɓa”.

Bayan dakarun sun kama ɗan na kamawa, wasu kuma sun tsere, sai su ka zaunar da su a harabar makarantar, inda su ka aske musu gashin tas.

Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da jami’in Sashen Fasahar Sadarwa ta Zamani na Hisba ɗin, Abdulwahab Said Ahmad, a shelkwatar ta da ke birnin Kano.

Ya ce an yi wa ɗaliban dake kammala jarrabawar gama sakandiren aski ne saboda wanda su ka yi a kawunansu ya sava da al’adar Hausawa da kuma tarbiyya.