Hukumar NAHCON ta kammala aikin hajjin bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai (NAHCON), ta sanar da kammala aikin hajji na bana.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta yi jigilar mahajjata na ƙarshe daga filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jiddah zuwa Nijeriya.

Hajiya Fatima Sanda, Shugabar Sashin Hulɗa da Jama’a na Hukumar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce, jirgin Nijeriya na ƙarshe na aikin Hajji na 2022, jirgin Azman Air mai alhazai 319 daga Kaduna da Kano da jami’ai daga jihohi daban-daban da NAHCON ya tashi daga filin jirgin sama na Sarki AbdulAziz na Jiddah a ranar 7 ga Agusta 2023 da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

Tafiyar ta nuna ƙarshen ayyukan Hajji na 2022 daga Nijeriya. Jirgin na ƙarshe na zuwa ne kwanaki shida gabanin wa’adin jigilar mahajjatan kamar yadda hukumomin Saudiyya suka gindaya, kuma kwanaki uku gabanin wa’adin da NAHCON ta tsara ya kasance 10 ga watan Agustan 2022. Sama da makonni uku da gudanar da aikin, an soke tashin jirage biyu ne kacal tare jinkirtawa na tsawon awa shida.

A bikin kawo ƙarshen aikin, shugaban hukumar NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya danganta nasarar kammalawar ga Ubangiji. Ya gode wa gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da ta ke bai wa hukumar Hajji.

Shugaban ya tabbatar da cewa, an samu ƙalubale a lokacin fita daga Nijeriya zuwa Saudiyya sakamakon ƙarancin lokaci da kuma wasu kura-kurai da ba a yi tsammani ba kamar batun IBAN da ya shafi wasu ’yan yawon buɗe ido. Duk da haka, hakan ya zaburar da Hukumar wajen ɗaukar darasi.

Ya jaddada cewa, hukumar za ta fara shiri da wuri kuma za ta fara tantance kamfanonin jiragen sama nan ba da daɗewa ba domin bai wa masu jigilar kayayyaki damar tsallake duk wani cikas da ba a yi tsammani ba cikin lokaci mai kyau.

Ya kuma jaddada cewa, Hukumar za ta tabbatar da cewa duk wata yarjejeniya ta kwangilar da aka sanya hannu ta cika kamar yadda aka amince.

A wani labarin kuma, an shirya liyafar cin abincin dare a ranar 6 ga watan Agusta domin karrama hukumar NAHCON da ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2023.

Shugaban Kamfanin Mutawif na Alhazai daga ƙasashen Afirka da ba na Larabawa ba, Ahmad Sindi ya yaba da aikin Hajjin Nijeriya a matsayin tawaga mafi muhimmanci a kamfanin. A cikin kalamansa ya ce, “Nijeriya na da matuar muhimmanci ga kamfanin”.

Ya koka da cewa, ba a yi wasu abubuwa kamar yadda kamfanin ke so ba amma ya tabbatar da cewa alhazan sun cancanci a yi musu hidima kuma a shirye su ke su bayar ba tare da la’akari da komai ba.

Don haka, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Hassan ya gabatar da buƙatu guda uku a wurin bikin na farko shi ne sadarwa a kan ƙa’idojin aikin Hajji na 2023, na biyu kuma duba tsarin ciyar da abinci a Masha’ir, na uku kuma shi ne neman a gaggauta warware matsalar toshewar IBAN da ta hana wasu Alhazai zuwa aikin Hajjin bana.

Shugaban ya kuma taɓo batun rashin isassun fili da kuma sanya alamar jin daɗi a Muna.

Da ya ke mayar da martani, Sindi ya tabbatar wa NAHCON cewa aikin Hajji na shekarar 2023 za a yi cikakken gyara saɓanin shirye-shiryen na bana. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa adadin aikin Hajji zai dawo kamar yadda ya ke a yanzu, don haka ya ba da shawarar cewa NAHCON ta fara aiki da ainihin adadi har sai an ba da umarni.

Ya kuma bayyana cewa, tuni ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta haɗa hannu da kamfanonin injiniyanci kan inganta kayayyakin aiki a Muna, Arafat da Muzdalifa.

Za a aiwatar da shirin cikin matakai. Duk da haka, kamfaninsa ya aike da wata shawara don aiwatar da shirin don amfanin alhazai ko da kuwa ci gaba wanda zai kasance na ɗan lokaci ne kafin aikin injiniyancin na ‘phasal’ ya isa shafinmu.