Fulaninmu na cikin wani hali a Jihar Edo, inji Sarkin Sarakunan Fulanin jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sarkin Sarakunan Fulanin Jihar Edo, Alhaji Muhammadu Sossa ya yi kira ga gwamnatin jihar Edo da ta yi wa Allah da AnnabinSa ta janye dokar da tasa na korar Fulani a jihar baki ɗaya nan da kwana biyar.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan hukuncin kwana 5 da gwamnatin ta ba kowane Bafulatani ya bar jihar.

Sarki ya ce a gaskiya ɗaukar wannan mataki zai cutar da Fulanin da ke zaune a dukkan faɗin jihar bisa ga yadda mafi yawan Fulanin dake zaune a jihar sun haura shekaru 30 zuwa 50 suna zaune a jihar ba tare da an samesu da wani laifi ba.

Basaraken ya ce mai zai hana a gaya masu laifin da suka yi kafin a koresu.

Sannan ya tabbatar da cewa su ba sa marawa duk wani ɓatagarin Fulani baya, kuma ba su yadda da ta’addanci ba kuma suna goyon bayan hukunta duk wanda ya yi laifi.

Tuni sarkin ya janyo hankalin gwamnati da ta ba su damar saurarensu maimakon ba su kwana biyar musamman a irin wannan yanayin mai cike da ƙalubale.

Shugaban ya ce, “Ina da tabbacin duk inda muka je babu wanda zai yarda da mu saboda yanayin da ake ciki na rashin aminci.”

Ya ce don haka yana son a sauraresu don su ji dalilin korar tasu bayan da yawan Fulani suna da gonaki da suka yi shuka kuma amfani ya yi girma sosai.

Kuma ya ce su a garesu jihar Edo jihar su ne tunda da yawansu a nan aka haifesu.

Bisa haka sarkin ya ce yana kira ga Gwamna da duk sauran masu faɗa a ji da su sa baki don gyara lamarin, ya ce ba dukkan Fulani suka zama lalatattu ba akwai masu tsoran Allah da kiyaye doka.

Ya ce yanzu haka suna da labarin an fara ƙona musu gidaje a wasu yankin, bisa haka sarkin ya nemi gwamnati ta duba wannan lamarin don ɗaukar mataki.