Makarantar Mariri Community ta shirya taron bankwana da ɗaliban zangon ƙarshe

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A ƙoƙarin ta na buƙasa ilimi mai inganci da tarbiyya. Makarantar Mariri Community Nursery and Primary and Secondary School.

Ta shirya wani gagarumin taro domin karramawa tare da Bankwana da ɗaliban da suka zo zangon Karatun su na ƙarshe a makarantar.

Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar 5 ga Agusta, 2022, a harabar makarantar da ke Unguwar Mariri ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin jihar Kano, ya samu halartar nanyan baƙi da ɗaliban makarantar.

Tun da farko da ya ke gabatar da jawabi a game da shirya taron ɗaya daga cikin daraktocin makarantar, Malam Ibrahim Yakub Idris, kuma Principal na farko a makarantar ya bayyana taron a matsayin wani abin alfahari da makarantar ta shirya kasancewar makarantar ta fara zama da gindinta.

Don haka ya yi kira ga iyayen yara da su rinƙa lura da makaranta kafin su saka yaran su, domin su tabbatar sun samu ilimi mai inganci da kuma tarbiyya.

Daga ƙarshe ya yaba da ƙwazon ɗaliban da suka zo zangon karatunsu na ƙarshe a makarantar.

A wajen taron dai an gabatar da jawabai da dama da su ke ƙarfafa wa yara a game da karatu.

Sannan kuma a wani ɓangare na taron an nishaɗantar da yara.

Baya ga haka an karrama ɗaliban da suka yi fice a fannoni da yawa waɗanda suka haɗa da ɗaliban da suka zo na ɗaya a vangaren lissafi. Da gasar ƙeke da ƙeƙe, wato “Debete” da waɗanda suka yi fice a ɓangaren tsafta, da waɗanda suka fi zuwa a kan lokaci da sauransu.

Ita dai wannan makaranta ta Mariri Community Nursery, Primary and Secondary School mutanen unguwar ne da su ke da kishin samar da ilimi ga yara suka kafa ta shekaru 19 da suka wuce.

Kuma a tsawon shekarun da ta yi ta yaye ɗalibai masu yawan gaske da suka tafi manyan makarantu suka ci gaba da karatu, wasu kuma sun samu aiki suna ci gaba da rayuwarsu a sakamakon ilimin da suka samu mai inganci tun daga tushe a makarantar ta Mariri Community Nursery, Primary and Secondary School. An dai yi taron an tashi lafiya.