Dora laifi kan wasu da ‘yan siyasar Amurka suka yi ya tsananata wariyar launin fata

Daga AMINA XU

MINA’Cartoons a wannan karo ya mai da hankali kan matsalar wariyar launin fata da ake fuskanta a Amurka.

A watan Maris na shekarar bara, Robert Allen L farin fata mai shekaru 21 a duniya ya yi ihu cewa: “Zan kashe dukkan ‘yan Asiya”, kuma ya harbe mutane 8 har lahira, ciki hadda mata ‘yan asalin Asiya 6. Abin baƙin ciki shi ne, irin wannan hari ya auku fiye da sau 500 a bana.

Bayan ɓarkewar cutar COVID-19, gwamnatin Amurka ta kasa ɗaukar matakan da suka dace, matakin da ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki a cikin gidanta, amma wasu ‘yan siyasa sun dora laifin ga wasu har abin ya tsananata matsalar wariyar fata a ƙasar, shi ya sa wasu mutane sun rasa rayukansu saboda gwamnatin ƙasar ba ta sauke nauyin dake wuyanta ba.

Mai zane: Amina Xu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *