Ta kashe kanta saboda mijinta zai ƙara aure

Daga WKAILINMU

Wata matar aure ta kashe kanta ta hanyar shan guba, saboda mijinta zai yi mata kishiya.

Matar, wacce su ke da ’ya’ya biyu tare da mijin nata, ta kwankwaɗi gubar ce bayan sun samu saɓani da shi kan shirinsa na ƙara aure, saboda Musulunci bai hana ba.

Wani ɗan uwan mijin marigayiyar mai suna Alhaji Lagbe Araoje, ya ce, “ranar Litinin da misalin ƙarfe 10 na safe ta samu saɓani da mijinta a waje, amma aka sasanta su. Daga baya mijin nata ya ba ta wata waya da ta ke so.”

“Bayan ’yan mintoci sai aka gan shi ya fito daga gidan yana kuka cewa matarsa tana amai. A hanyarmu ta kai ta asibiti ta riqa roƙon shi ya yafe ma ta, tana bayyana cewa wani garin hoda da ake kira DDT ko Sniper ta sha.

“Daga baya Allah ya yi ma ta cikawa a asibiti da misalin ƙarfe 12 na rana,” a Babban Asibitin Ilori da ke Jihar Kwara.

Wani mai shagon sayar da maganon ƙwari a yankin da abin ya faru ya tabbatar cewa marigayiyar ta sayi Sniper a kantinsa.

Amma wata wadda ta ce abokiyar karatun mamaciyar ce, ta yi zargin cewa surukar mai rasuwar ce ta sanya ma ta guba, saboda sun samu saɓani kan addinin da marigayiyar wadda Kirista ce.