Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida a majalisar wakilai Abdullahi Aliyu Ahmed ya taya gwamna Dikko Raɗɗa murnan cika shekara 55 da haihuwa.
Ɗan majalisar mai wakiltar musawa da matazu ya bayyana gwamna Dikko Raɗɗa a matsayin abin koyi,wanda a kullum ƙoƙarinsa gina sabuwar Jihar Katsina.
Bayanin haka na ƙunshe ne a wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun maitimaki na musamman a kan yaɗa labarai na ɗan majalisar Mr Francis Sardauna, ya ce Dikko Raɗɗa jagora ne abin koyi.
“Malam Dikko Raɗɗa mutum ne mai karamci da nuna sanin yakamata wajen gudanar da mulkin Jihar Katsina da dama tun yana shugaban ƙaramar hukumar Charanchi haka yake” Dujuman yace.
Ɗan majalisar wanda har wala yau, yayi addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da hikimar cigaba da gudanar da mulki cikin adalci kamar yadda ya faro domin gani jihar Katsina ta bunƙasa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba gwamnan goyon baya musamman a ƙoƙarin da yakeyi na magance matsalar tsaro a jihar.
Dujuman Katsina ya tabbatar wa gwamn Dikko Raɗɗa da cikakken goyon bayan ɗaukacin ‘yan majalisar ƙasa da ke wakiltar jihar .
Ya ce su a majisar wakilai da na dattawa suna iya ƙoƙarin su wajan gabatar da ƙudiri na ganin jihar Katsina ta sami zaman lafiya dawamamme da bunƙasar tattalin arziki.
