Duk Kannywwod ba wanda ya kai ni kayan aiki, inji Rashida Maisa’a

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano.

Fitacciyar jaruma kuma furodusa a masana’antar shirin finafinan Hausa ta Kannywood, Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a, tana ɗaya daga cikin jarumai mata da suka daɗe a na damawa da su a cikin harkar fim kafin daga baya ta juya akala ta zama ‘yar siyasa. Abubuwa guda biyu sun faru a wannan lokacin, wanda ya sa a ke tambayar ko dai jarumar ta dawo harkar fim ne bayan tsawon lokacin da ba a ganinta? Abu na farko dai zaɓar ta da aka yi a matsayin Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar ‘Arewa Film Markets Associations Of Nigeria’ (AFMAN). Na biyu kuma ganin ta da aka yi a cikin wani sabon fim da su Jarumi Sani Danja suka shirya, wanda ta fito a matsayin jaruma. Kan haka ne Wakilin Blueprint Manhaja ya tattauna da ita. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance:

MANHAJA: Rashida Adamu, an samu tsawon lokaci ba a ganin ki a harkar fim wanda hakan ta sa a ke ganin kamar kin bar harkar, kin bar wa na baya, amma dai a ɗan wannan lokacin an gan ki wajen aikin har ma kin fito a matsayin jaruma. 
RASHIDA: To, alhamdu lillahi. Daman ba na daina fim ba ne ko da an daina gani na, amma dai a yanzu da wannan dama ta samu a gare ni wadda aka zaɓe ni a matsayin Mataimakiyar Shugaban Ƙungiyar Arewa Film Markets Associations Of Nigeria, to ya kamata a rinƙa gani na, amma dai kafin wannan duk da Ina yin fim a gaskiya sai na kai sama da shekara biyu ma ban yi ba. To amma daga yanzu na dawo zan ci gaba da yi saboda matsayin da na ke riƙe da shi duk da cewar ba kowanne fim zan yi ba, don haka ko da zan yi fim sai na zaɓo kamfanin da zan yi wa aiki don haka sai na duba fim mai ma’ana, wanda zai kawo ci gaba ba na shiririta ba, don haka ko a yanzu na yi finafinai a ‘yan kwanakin nan, sai dai ba su fi guda biyu ba, akwai fim ɗin Sharukan, mai suna ‘Daga Dinner’, sai kuma na su Sani Danja mai suna ‘Matan Alhaji’. Kuma shi fim ne mai dogon zango, kuma aka haɗa jaruman Kudu da Arewa don haka Ina shiga irin waɗannan finafinan wanda ka san mutum kuɗin sa ya zuba masu yawa domin ya shirya fim mai inganci mai ma’ana. Kuma a yanzu ma akwai finafinan da aka kawo mini da zan yi nan gaba, saboda a matsayina da na ke shugabancin abin ya kamata na kasance a cikin sa ana damawa da ni. 

Amma kuma ba kya ganin harkokin ki na tafiye-tafiye da na siyasa ba za su ba ki damar da za ki rinƙa zuwa aikin fim ba? 
Eh, tafiye-tafiye da na ke yi da suka shafi kasuwanci na da kuma harkar siyasa, ka ga daman tun a baya da aka sanni a harkar fim ni ‘yar kasuwa ce, kuma ba daina wa na yi ba. Sannan kamar irin abubuwan nan na siyasa za ka ganni yau Ina wannan gari, gobe Ina can, to shi ma ba zai hana ni harkar fim ba, domin abu ne na tsari, don haka zan tsara komai yadda ya kamata. Don gaskiya duk abin da zan yi a duniya Ina alfahari da fim, domin ni fim babu abin da bai yi mini ba, ko ɗaukakar da na yi ta dalilin fim ne da na shiga sai Allah ya ƙaukaka ni. Kuma ta dalilina akwai waɗanda suka yi suna a cikin harkar suka zama wani abu, kuma har yanzu Ina alfahari akwai yaran da mu ke koya mu su ‘Camara’, kamar ƙane na Abubakar Adamu Abdullahi J Boy kowa ya san shi a harkar fim uwar mu ɗaya da shi a yanzu a harkar Camara dai idan bai zo na ɗaya ba zai zo na biyu. To ni na jawo shi na sa ya koyi Camara, kuma mu ke samun yara mu na koya mu su, a yanzu a wajen mu mu na da mutune sama da ɗari da mu ka koya mu su, mu ka yaye su, a yanzu sun koma suna cin gashin kansu su na koyar da wasu, to ka ga abin alfahari ne a ce ka gina mutum yana riƙe da kan sa. Don haka ko me zan yi a duniya, gaskiya fim ne gaba da shi. 

A baya an san ki a matsayin Furodusa. Ko za ki dawo ki cigaba da shirya fim? 
Ai har gobe da jibi ban daina ba, domin ko finafinan nan masu dogon zango mu na shirya su saboda a kamfaninmu mu ke shiryawa, da ya ke ƙane na shi ya ke tafiyar da abin, sai dai in an gama ya zo ya sanar da ni, don haka kamfani ne da mu sai dai a yi da sunan kamfani ba kamar a baya da na ke yi da suna na ba, domin ba cika baki na yi ba, duk a Kannywwod babu wanda ya kai mu kayan aiki wanda a ke zuwa ana karɓar haya don haka kusan wannan kamfanin shi ne yake riƙe da ni da ‘yan’uwa na, don Ina riƙe da mutum sama da a shirin a gidana ‘yan’uwa da marayu, akwai wanda su ke jini na ne, kuma akwai marayu da na ke riƙe da su da cin su da shan su da karatunsu duk ni na ke kula da su. 

To, idan mu ka koma ɓangaren siyasa da a yanzu an fara shiga cikin ta, mece ce makomar siyasar ‘yan fim a zaɓe mai zuwa? 
Eh, haka ne, mu dai a harkar siyasa kowa ya san mu tun a lokutan baya sunanmu ya bazu a duniya komai hassadar mutum dai ya sani, tun da mun san yadda za mu shirya mutum ya ci zaɓe kuma mun san yadda za mu shirya mutum ya faɗi saboda muna da jama’a a ƙasa, sakamakon kyakyawar alaƙar mu da mutane, saboda kwatanta gaskiya da ba su haƙƙin su, don haka su ‘yan fim su sani siyasa kowa yana da ra’ayin sa, don haka kada ra’ayin ka ya haɗa ka fɗa da abokin sana’ar ka, saboda siyasa za ta ƙare, fim kuma ba zai ƙare ba, domin fatan mu ‘ya’yanmu da jikokinmu su gaji wannan sana’ar ta mu ta fim, don haka Ina ba da shawara, duk in da za ka ƙaru ka samu ka je ka nemi abin da za ka samu, domin ita siyasa ba don lada a ke yin ta ba, don a samu ake yin ta, amma ta hanyar siyasar za samu harya da za ka samu Aljanna idan ka kwatanta gaskiya, kuma za ta iya saka ka wuta idan ka yi rashin gaskiya, don haka Ina so idan mun zo harkar fim ya zama kan mu a haɗe yake, idan kuma aka tafi filin siyasa, a buga siyasa, amma ba da gaba ba. Ina fatan abokan sana’a ta za mu yi harkar siyasarmu cikin tsari.

To, madalla mun gode.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *