APC za ta gudanar da babban taronta a Maris

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC mai mulki ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ta bayar da sanarwar ya zuwa ranar 26 ga Maris mai zuwa za ta gudanar da babban taronta na ƙasa.

Sanarwar hakan na ƙushe ne cikin wata wasiƙa da APC ta aike wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) dangane da zaɓen shiyyoyi da za ta gudanar.

Sakataren APC na ƙasa, Dr John Akpanudoedehe, shi ne ya bada sanarwar tsayar da sabuwar ranar zaɓen ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani taron sirri, tare da cewa shirye-shiryen babban taron nasu za su kankama ne ran 24 ga Maris, 2022, yayin da kuma za a gudanar da zaɓukan shiyyoyi kafin ranar babban zaɓen wanda zai gudana ran 26 ga Maris 2022.