Duniya rawar ‘yammata: BUA ya kere arzikin Ɗangote a watan Afrilun bana

Daga AMINA YUSUF ALI

AbdulSamad Rabiu, hamshaƙin ɗan kasuwa a Nijeriya, kuma mutum na biyu ma fi dukiya a ƙasar ya buga tarihi a watan Afrilun shekarar bana ta 2023 a cewar sakamakon binciken kwanan nan da Forbes suka gudanar.

Ƙarfin arzikin na Abdulsamad Rabi’u ya yi tashin gwauron zabi zuwa Dalar Amurla biliyan $8.6 a ƙarshe watan Afrilun na bana. Wato dai an samu ƙaruwar maƙudan kuɗi har Dalar Amurka biliyan $300 wato kwatankwacin Naira biliyan 138.14 musamman idan aka kwatanta dukiyarsa da dalar Amurka biliyan $8.3 da take a 1 ga watan Afrilu, 2023.

Wannan ya nuna cewa, Abdulsamad Rabiu ya samu kwatankwacin Naira biliyan 4.6 kowacce rana a cikin tsahon kwanakin wata 30 na watan Afrilu, 2023.

Hakazalika, alƙalumma sun nuna cewa, wannan tashin gwauron zabin da dukiyar tasa ta yi, ya sa ya kere attajiri Ɗangote a dukiya, a cikin watan na Afrilu. Domin shi Ɗangote dukiyarsa ta qaru ne da Dalar Amurka miliyan $100 (Naira biliyan 46.04) ne kacal a watan na Afrilu.

Sai dai sakamakon binciken na Forbes ya rawaito cewa, dukiyar Ɗangote ta haura zuwa dalar Amurka biliyan $13.6 ranar 30 ga Afrilu, wto saɓanin yadda take a dala biliyan $13.5 a ranar 1 ga Afrilu.