EFCC na neman matar Emefiele ruwa a jallo bisa zargin almundahana

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta ce tana neman matar tsohon Gwamnan CBN, Margaret Emefiele da wasu mutum uku ruwa a jallo a kan batun da ya shafi almundahana.

Majiyarmu ta bayyana cewa a daren Juma’ar da ta gabata EFCC ta sanar da neman da take yi wa Mrs Emefiele da Mr Eric Odoh da Anita Omoile tare da mijinta Jonathan Omoile.

Hukumar na neman waɗanda lamarin ya shafa ne bisa zargin haɗin baki da tsohon Gwamnan na CBN “wajen karkatar da maƙudan kuɗi mallakar Gwamnatin Tarayya wanda hakan ya sa suka mallaki kuɗi ta hanyar ƙarya da sata wanda ya saɓa wa Sassa na 411, 287 da 314 na Dokar Manyan Laifuka na Jihar Legas.”

Wani bayanin EFCC da majiyarmu ta samu a baya, ya nuna ana tuhumar tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele bisa almundahanar Naira biliyan 1.8 da kuma Dala miliyan 6.2.

Kawo yanzu kuma a karo na uku, Gwamnatin Tarayya ta sabunta tuhuma a kan Emefiele.

A sabuwar tuhuma ta baya-bayan da EFCC ke yi wa Emefiele wadda ta gabatar a gaban Mai Shari’a Hamza Muazu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, hukumar na zargin tsohon Gwamnan CBN ɗin da yin shigar burtu a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya wajen karɓara kuɗi har Dala miliyan illegally 6.2.

Sabuwar tuhumar mai lamba CR/577/2023, ta nuna Emefiele ya haɗa baki da wani mai suna Odoh Ocheme a ranar 8 ga Fabrairun 2023 wajen karɓar Dala Miliyan 6.2 daga CBN inda ya fake da cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ya buƙaci a bada kuɗin a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairu, 2023 da kuma lamba SGF.43/L.01/201.

By Editor