AFCON 2023: Tinubu zai halarci kallon wasan ƙarshe da Nijeriya za ta buga

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci kallon wasan ƙarshe da Nijeriya za ta buga a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) 2023 da ke gudana a Côte d’Ivoire.

Ya zuwa ranar Lahadi ake sa ran Nijeriya da Côte d’Ivoire za su fafata a wasan ƙarshe na gasar wanda za a buga a Abidjan.

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta CAF, Patrice Motsepe, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya shirya ranar Juma’a a Abidjan.

Za a buga wasan ƙarshen ne a filin wasannin motsa jiki na Alassanne Ouattara, Ebimpe, Abidjan.

Tuni dai ‘yan Nijeriya suka shiga zumuɗin ganin wannan rana domin shaida yadda wasan zai kaya tsakanin Nijeriya da abokiyar karawarta, Côte d’Ivoire wadda kuma ita ce mai masaukin baƙi.

Super Eagles ta Nijeriya ta samu nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a gasar ne bayan da ta yi galaba a kan Afirka ta Kudu a wasan ƙarshen da suka buga.

By Editor