Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe
An bayyana Ministan Sadarwan Zamani da Tattalin Arziki na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Al-huda-hudan ilimi a wannan zamanin.
Babban sakatare a hukumar kula da jami’o’in Nijeriya (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na Mataimakan Shugabannin jami’o’in Gwamnati na Nijeriya (VC Retreat) da aka gudanar, inda ya jinjina wa Farfesa Pantami a kan irin baiwarsa ta ilimi da yake da ita.
Ya ƙara da cewa, Isa Ali gangaran ne a ɓangaren ilimin addini da na zamani wanda haziƙancinsa ya sa aka bayyana shi da Al-huda-huda, inda ya bayyana cewa a matsayin Al-huda-huda ganin yadda ya gabatar da wata kasida da ilimi ya bayyana.
Ya ce, “tun kafin Isah Ali Pantami ya zama Farfesa yake da baiwa ta musamman har zuwa yanzu da ya zama Farfesan farfesosi.
A cewarsa, ba kowane Farfesa ne zai yi kamar Isah Ali Pantami ba domin haziƙi ne, don haka daga yanzu ya zama Al-huda-huda.
Ya ci gaba da cewa mukalar da Isah Ali ya gabatar sai da kowa a wajen taron ya kwankwaɗi ilimi ya ƙoshi domin ya fito da tsari na zamani kan tsare-tsaren darussan da ake koyarwa a jami’o’in ƙasar nan daga tsohuwar hanya zuwa hanya ta zamani.
Ya hori shugabannin jami’o’in da cewa su tattara bayanan da Pantami ya yi a waje guda a buga a mujalla ko a turawa mutane kaitsaye a akwatin saƙonni na imel don a dinga nazari akai ana ƙara samun ilimi.
A gefe guda wajen bunqasa tattalin arziki ta hanyar sadarwar zamani, Babban Daraktan Galaxy Back bone, Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ta bakin mai taimaka masa a ɓangaren sadarwa, Tasiu Mohammad Pantami, cewa ya yi zuwan ministan, arzikin Nijeriya ya bunƙasa fiye da shekarun da suka gabata.
Tasiu Pantami, ya ce Isah Ali Pantami, minista ne da ba a taɓa yin kamarsa a tarihin Nijeriya ba, wanda ya ɗaga Nijeriya a idon duniya a ɓangaren tattalin arziki kuma ya bar tarihin da ba za a taɓa mantawa da shi ba.
