Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙara nanata aniyar gwamnatinsa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta, yana mai cewa ko kaɗan bai zai raga wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce manyan hafsoshin tsaron ƙasar na iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga a ƙasar.
Ya kuma jajenta wa tsohon shugaban Jam’iyyar PDP, Adamu Muazu, saboda kashe ɗan uwansa da ‘yan bindiga suka yi tare kuma da kame ‘yar uwarsa.
Yayin da yake bayyana ‘yan bindigar a matsayin maƙiya al’umma, Shugaba Buhari ya ce ya kaɗu matuqa da wannan kisan.
Ya ƙara da cewa: ”Na yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin kashe ɗan uwanka, tare da kama ‘yar uwarka. Wannan masifa kullum ƙaruwa take yi a ƙasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku baƙin-ciki.
”Matsalar tsaro ita ce babban abin da na sa a gaba, na kuma umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar da su yi iya bakin ƙoƙarinsu, domin kawo ƙarshen wannan matsala da lasarmu ke ciki,” inji Buhari.
Waɗannan kalaman na zuwa ne bayan ‘yan bindigar da suka sace gomman fasinjojin jirgin ƙasan nan na Abuja zuwa Kaduna, tun ranar 28 ga watan Maris ɗin da ya gabata, sun sake fitar da wani sabon hoton bidiyo da ke nuna mutanen da ake garkuwa da su cikin mummunan yanayi.
A cikin bidiyon mai tsawon kusan minti goma sha ɗaya, an ga ‘yan bindigar na lakaɗa wa fasinjojin maza dukan tsiya da itace.
